Yaya Toure na son tsawaita kwantiraginsa da City

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yaya Toure na kakarsa ta bakwai a Etihad

Dan wasan tsakiya na Ivory Coast, Yaya Toure na son a tsawaita masa kwantiraginsa a City.

Dan wasan mai shekara 34, kwantiraginsa da kungiyar zai kare ne a karshen kakar wasa ta bana.

Toure, dai a baya ya nuna kamar zai bar kungiyar, bayan da aka ki sanya shi cikin tawagar kungiyar da za su buga gasar Zakarun Turai, kuma ba a fara buga gasar Premier da shi ba, sai a watan Nuwamba.

Sai dai yayin da Toure ke fatan ci gaba da murza leda a City, Shi kuwa dan wasan baya na kungiyar Pablo Zabaleta, barin City zai yi, bayan shafe kakar wasa tara a kungiyar.

Kungiyar dai, za ta karrama Zabaleta, a wasansu da West Brom, kuma na karshe da kungiyar za ta yi a gida, a wannan kakar wasa, ranar Talata.

Zabaleta, wanda ya koma City daga Espanyol a watan Agustan 2008, shi ne dan wasa na uku mafi dadewa a kungiyar bayan Joe Hart da Vincent Kompany.

Ya yi wa kungiyar wasa sama da 322, ya ci kofin Premier sau biyu, da kofin FA guda daya, da kuma kofin Carlin guda biyu.

Labarai masu alaka