Martin zai yi ritaya daga ƙwallon ƙafa

Martin Demichelis Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Martin na Man City daga shekarar 2013 zuwa 2016

Tsohon dan wasan baya da tsakiya na Manchester City, Martin Demichelis ya bayyana cewa zai yi ritaya daga kwallon kafa, yana mai shekara 36.

Dan wasan dan asalin Argentina ya buga wa City wasa daga shekarar 2013 zuwa 2016. Ya kuma taimaka wa kungiyar wajen lashe kofin gasar Premier ta kakar 2013-14, da kuma kofin Carlin guda biyu.

Ya kuma dauki kofin Bundesliga sau hudu tare da Bayern Munich.

Haka kuma dan wasan na cikin tawagar da ta wakilci kasar ta Argentina zuwa gasar kofin duniya ta shekarar 2014, da aka yi a kasar Jamus.

Labarai masu alaka