Juventus ta sha mamaki a hannun Roma

Juventus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Juventus na fatan lashe kofin Serei A sau shida a jere

Yanzu dai saura maki hudu tsakinta da Roma wacce ke ta biyu a kan tebur, inda ya rage wasa biyu a kammala gasar. Sai dai za su sami damar daukar kofin idan suka doke Crotone ranar Lahadi mai zuwa.

Kafin ranar Lahadin dai, za ta kara da Lazio, a wasan karshe na kofin Coppa Italiya, ranar Laraba mai zuwa.

Juventus din ce dai ta fara daga ragar Roma ta hannun Mario Lemina, Sai dai Daniele de Rossi, da Stephan El Shaarawy da kuma Radja Nainggolan sun kara jaddada wa Roma fatan da take da shi.

Har yanzu dai kungiyar ka iya daukar kofin, kuma tana da damar yin hakan idan ta doke Crotone, ranar Lahadi Mai zuwa a gaban dumbin magoya bayanta.

Za ma ta iya daukar kofin ranar Asabar, idan Roma ta yi rashin nasara a hannun Chievo, kuma Napoli wacce ke mataki na uku ta kasa doke Fiorentina a gidanta.

Daga wannan matakin ne, Juventus za ta iya hasashen wasanta na karshe na gasar Zakarun Turai, inda za ta fafata da Real Madrid, ranar 3 ga watan Yuni a birnin Cardiff na kasar Ingila

Labarai masu alaka