Ba za mu saki jiki ba-Zidane

Zinidine Zidane
Image caption Zidane na fatan zama kocin kungiyar na farko da ya dauki Laliga tun 2012

Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane, ya ce 'yan wasan kungiyar ba sa maganar daukar kofi duk kuwa da damar yin hakan da suke da ita, yayin da suke da sauran wasa biyu.

Madrid wacce ke mataki na biyu a kan tebur tana da maki daidai da na Barcelona, wacce ke kan gaba saboda bambancin yawan nasara a kan 'yan Madrid din, wadanda suke da kwantan wasa daya.

Idan Madrid ta yi nasara a kan Celta Vigo ranar Laraba, da kuma Malaga ranar Lahadi, za ta dauki kofin a karon farko tun shekarar 2012.

"Wasan Celta Vigo kawai muke tunani" in ji Zidane.

Kocin dan Faransa na fatan jagorantar kungiyar wajen lashe kofunan Laliga da kuma na Zakarun Turai, idan ta doke Juventus ranar 3 ga watan Yuni a birnin Cardiff.

Amma da farko sai sun mayar da hankali wajen doke Celta Vigo wacce ke matsayi na 13, a kwantan wasa da za su buga Larabar nan

"Ba wanda ke maganar daukar kofin a dakin sanya kayanmu na wasa." in ji Zidane, wanda ya jagoranci kungiyar lashe kofin Zakarun Turai a shekarar da ta gabata a kakarsa ta farko a kungiyar.

"Ba wanda ke jin zai dauki kofi, za mu ci gaba har ya zuwa mintin karshe na wasan karshe. Ba mu dauki wani kofi ba saboda haka ba za mu sakankance ba."

Ana sa ran fara wasa da Cristiano Ronaldo, wanda aka hutar da shi a wasanni hudu da kungiyar ta yi a waje.

Gareth Bale ba zai buga wasan ba, saboda jinyar ciwon sharaba da yake yi, haka kuma Pepe, da Dani Carvajal, da kuma James Rodriguez, ba za su buga wasan ba suma saboda suna fama da jinya.

Labarai masu alaka