Mazzari zai bar Watford kafin lokacinsa

Walter Mazzarri Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Walter Mazzarri zai bar Watford bayan shekara daya a kwatiraginsa na shekara uku

Kociyan Watford Walter Mazzarri zai bar kungiyar bayan wasan karshe da za ta yi ranar Lahadi a gidan Manchester City, duk da cewa bai cika wa'adin kwantiraginsa ba na shekara uku.

Mazzarri dan Italiya mai shekara 55 ya kama aikin kociyan kungiyar wadda take matsayi na 16 a teburin Premier, tsawon kasa da shekara daya.

Shugaban kungiyar Scott Duxbury ya ce an cimma matsaya ne kan tafiyar kociyan bayan taron da hukumar kungiyar ta yi da shi a kan burinta.

Kociyan kungiyar na gaba zai kasance na tara a cikin shekara biyar, kuma zai kasance na takwas tun bayan da iyalan gidan Pozzo 'yan Italiya suka sayi kungiyar a 2012.

Rashin nasarar da kungiyar ta yi ranar Litinin a gidan Chelsea da ta ci ta 4-3, shi ne karo na biyar a jere da take shan kashi, ko da yake ta kauce wa hadarin faduwa daga Premier, kuma tana da maki shida tsakaninta da rukunin faduwar, yayin da ya rage wasa daya a kammala gasar.

A watan Mayu na 2016 Watford ta dauki tsohon kociyan na Inter Milan Mazzari domin ya yi mata aiki na tsawon shekara uku, daga watan Yuli bayan da Quique Sanchez Flores ya bar aikin.

Wasu na ganin kociyan ba shi da kyakkyawar fahimta tsakaninsa da wasu 'yan wasan kungiyar.

Masu fashin bakin wasanni na hasashen tsohon kociyan Leicester Claudio Ranieri da na Hull City Marco Silva a cikinsu wani zai iya maye gurbin Mazzarri.