Europa: Man Utd za ta yi asarar fan miliyan 50 idan Ajax ta doke ta

Kociyan Manchester United Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Man United karkashin jagorancin Jose Mourinho tana matsayi na shida a Premier

Manchester United za ta yi asarar fan miliyan 50 idan har ta bari Ajax ta doke ta a wasan karshe na cin kofin Europa ranar 24 ga watan Mayu.

Wasan da za a yi a birnin Stockholm shi ne damar kawai da ta rage wa kungiyar ta zuwa gasar Zakarun Turai ta Uefa.

Idan har United ta kasa samun damar zuwa gasar ta Zakarun Turai ta Uefa a karo na biyu a jere hakan zai sa ta biya tarar fan miliyan 21 bisa yarjejeniyar da kamfanin Adidas ya kulla ta fan miliyan 750 ta daukar nauyin kungiyar tsawon shekara 10.

Amma kuma idan har kungiyar ta yi nasarar samun gurbin buga gasar ta Zakarun Turai mai zuwa, to za ta samu har fan miliyan 30.

Sannan kuma duk kungiyar da ta yi nasara a wasan na mako mai zuwa za ta samu ladan fan miliyan shida da rabi, wadda ta yi rashin nasara kuwa za ta samu fan miliyan uku da rabi.

Babban jami'in kudi na Manchester United Cliff Baty, ya ce kungiyar takan samu tsakanin fan miliyan 40 zuwa 50 idan ta samu zuwa gasar Zakarun Turai ta Uefa sabanin fan miliyan 15 zuwa 20 da ake sa ran za ta samu a gasar kofin Europa.