Draxler na son Ozil ya koma PSG

Julian Draxler a wasan PSG Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Julian Draxler ya koma PSG ne daga Wolfsburg a watan Janairu a kan fan miliyan 35 da rabi

Ya kamata dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil ya koma Paris St-Germain, in ji abokin wasansa a tawagar Jamus Julian Draxler.

Draxler, wanda ya ce ya ki amsa gayyatar kungiyoyin Premier, a maimakon haka ya zabi tafiya PSG a watan Janairu, ya ce Ozil zai ji dadin zama a Paris.

A wata hira dan wasan ya gaya wa BBC cewa, zai so a ce kullum suna wasa tare, domin yana jin dadin hakan a lokacin atisaye ne ko kuma a wasannin tawagar Jamus, ''saboda a wurina babban dan wasa ne''.

Da aka tambaye shi ko yana ganin Ozil din zai koma Paris, sai Draxler ya ce : ''Eh, ina ganin gwanin dan wasa ne da zai taimaka wa duk wata kungiya ta duniya, kuma ina ganin zai ji dadin zamansa a Paris da ma yi wa PSG wasa.

Ozil yana da sama da shekara daya ne kawai a kwantiraginsa da Arsenal, yayin da kociyan kungiyar Arsene Wenger ya ce an dakatar da tattaunawa da dan wasan mai shekara 28 har zuwa bazara.

Draxler, mai shekara 23, ya ce ba kudi ba ne ya sa ya yanke shawarar tafiya PSG maimakon wata kungiya ta Premier a watan Janairu, shawara ce kawai ta radin kansa.