Ingila: Za a dakatar da duk dan wasan da ya fadi da gangan

Gaston Ramirez na Middlesbrough ya fadi da gangan a gidan Bournemouth Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An ba wa Gaston Ramirez na Middlesbrough katin gargadi daya a gidan Bournemouth saboda faduwa da gangan, kafin a kara masa daya a kore shi

Daga kaka mai zuwa duk dan wasan da a Ingila ya fadi da gangan domin yaudarar alkalin wasa don su samu fanareti ko wata dama za a dakatar da shi.

A bisa sabuwar dokar da hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta bullo da ita, a babban taronta na shekara-shekara a ranar Alhamis din nan, wani kwamiti na musamman ne zai rika nazarin bidiyon wasannin da aka yi a karshen mako, a duk ranar Litinin domin gano irin wannan laifi na yaudarar alkalin wasa, inda dan wasa kan fadi kamar an yi masa keta.

A yayin nazarin hoton bidiyon wasannin duk dan wasan da 'yan kwamitin suka samu da laifi za a dakatar da shi daga buga wasanni.

Kwamitin zai kunshi tsohon alkalin wasa daya da tsohon kociya da kuma tsohon dan wasa daya.

Laifin da za a yi hukunci a kansa shi ne wanda dan wasa ya yi nasarar yaudarar alkalin wasa har ya ba kungiyarsa fanareti ko aka kori dan wasan da ya yi wa sharrin ya yi masa ketar, ta hanyar ba da katin gargadi biyu ko jan kati kai tsaye.

Sabon tsarin na bukatar samun amincewar hukumar gasar Premier da hukumar lig din Ingila (EFL), da kuma kungiyar kwararrun 'yan wasa ta Ingila.

Tun a shekara ta 2011 ake fara aiwatar da irin wannan doka a wasannin kwallon kafa a Scotland.

Hukumar ta ce ta bullo da wannan hukunci ne bayan tattaunawa da ta yi da masu ruwa da tsaki a harkar wasan kwallon kafar a Ingila, a watannin da suka gabata.

Hukumar kwallon kafar ta Ingila ta kuma sanar da cewa a amince da wasu sauye-sauye da ta kawo shawarar bullo da su a watan Maris, sakamakon sukan da ake yi kan yadda ake tafiyar da ita.