Na amince in dambata da Mayweather - McGregor

Conor McGregor Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun a 2016 ake yada jita-jitar cewa Conor McGregor zai dambata da Floyd Mayweather

Zakaren damben boksin ajin marassa nauyi na UFC Conor McGregor ya yi ikirarin cewa ya rattaba hannu a bangarensa na yarjejeniyar dambatawa da tsohon zakaran duniya Floyd Mayweather.

Tun a shekarar 2016 ne ake radi-radin damben tsakanin McGregor dan Ireland da Mayweather bayan da McGregor ya yi nasarar doke Eddie Alvarez ya zama zakaran na UFC na duniya.

McGregor mai shekara 28 ya ce yanzu komai ya rage ga Ba'amurke Mayweather mai shekara 40, da mai ba shi shawara AlHaymon.

Shugaban kamfanin na UFC, da ke shirya damben boksin din da ake yi hannu da kafa Dana White, ya tabbatar da maganar ta McGregor ta amincewa a yi damben, kuma ya ce duk wata ganawa da za a yi da bangaren Mayweather ta dambatawa ce kawai ba wani dogon-turanci ba.

Masu fashin bakin damben boksin da dama na shakkun ko McGregor zai iya karawa da Mayweather, wanda ya yi ritaya a watan Satumba na 2015, ba tare da an taba doke shi ba a dambe 49 na kwararru da ya yi.