Tennis: Sharapova ta samu damar shekara biyu ta wasan Birmingham

Maria Sharapova Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yanzu Maria Sharapova ita ce ta 211 a jerin gwanayen tennis mata na duniya

Tsohuwar gwanar wasan tennis ta daya a duniya Maria Sharapova ta kulla yarjejeniya da hukumar kwallon tennis ta Ingila, domin ta shiga gasar Aegon Classic ta Birmingham tsawon shekara biyu.

A watan Yuni ne aka ba wa tsohuwar gwarzuwar mai shekara 30, wadda sau biyar tana cin kofin manyan gasar tennis na duniya, dama ta kai tsaye ta shiga gasar, bayan ta yo kasa a jerin gwanayen na duniya, bayan hukuncin dakatar da ita wata 15 saboda amfani da maganin kara kuzari da aka haramta.

Sai dai kuma hukumar kwallon tennis din ta Ingila LTA, ba za ta ba wa 'yar wasan ta Rasha kudin ladan shiga gasar ba.

A gasar Australian Open ta 2016 ne aka dakatar da Sharapova, sakamakon samunta da laifin amfani da wani maganin ciwon zuciya, ko da yake kotun sauraron kararrakin wasa ta duniya ta ce ba da niyya ta yi amfani da maganin ba, da nufin kara kuazari.

Zakaran tennis din na daya a duniya Andy Murray da wasu 'yan wasan mata da dama sun ce bai kamata a ba wa duk wanda ya kammala hukuncin dakatarwar laifin amfani da abubuwan kara kuzari, damar shiga gasa kai tsaye ba.