Uefa ta daina bikin mika kofi a kan bene sai a fili - Čeferin

Babban filin wasa na Wales Hakkin mallakar hoto Uefa
Image caption A babban filin Wales za a yi karon karshe na Zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Juventus

Hukumar Kwallon Fafa ta Turai ta ce daga wannan shekarar za a rika ba wa kyaftin din duk kungiyar da ta ci wata gasarta ta kungiyoyi ko ta kasashe kofi a cikin fili maimakon kan bene kamar yadda shugabanta Aleksander Čeferin ya sanar.

Shugaban hukumar ta Uefa ne zai bayar da kofin ga kyaftin din duk kungiyar da ta yi nasara a fili, a karawar karshe ta kofin Europa a Stockholm tsakanin Manchester United da Ajax ranar 24 ga watan Mayu.

Haka kuma a gasar Zakarun Turai ta mata ta Uefa a filin wasa na Cardiff City ranar 1 ga watan Yuni da kuma wasan karshe na kofin Zakarun Turai na Uefa tsakanin Real Madrid da Juventus a babban filin wasa na Wales ranar 3 ga watan Yuni.

Cikin kasa da minti biyar kacal za a rika hada dandamali na musamman da za a rika kafawa domin bikin bayar da kofin da sauran kyautuka.

An dawo da wannan tsarin ne domin ba wa dukkanin 'yan kallo da ke filin damar ganin shagalin mika kofin da kayu, sannan su ma masu kallo a talabijin su ga bikin yadda ya kamata.

Bayan hakan ma kuma shugaban na Uefa ya ce yin hakan wata alama ce, ta mutunta 'yan wasan, kasancewar filin shi ne fagen dagarsu, saboda haka abu ne da ya kamata a ce jami'ai sun sauko daga bene su zo wurin 'yan wasan, su girmama su da ba su kofin da kuma lambobin yabo.