Europa: Mourinho ya koka da rashin samun taimakon hukumar Premier

Jose Mourinho a wasan United da Southampton Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Man United ta yi 0-0 a gidan Southampton a wasanta na kusa da karshe na Premier ranar Laraba

Kociyan Manchester United Jose Mourinho ya ce abin takaici ne yadda hukumar gasar Premier ba ta damu ta taimaka wa kungiyoyin Ingila da ke gasar Turai ba.

United za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasansu na karshe na Premier ranar Lahadi, kwana uku kafin wasansu na karshe na Kofin Turai na Europa.

Idan ta yi nasara a kan Ajax a wasan na Stockholm ranar Laraba, kungiyar ta Mourinho ta samu gurbin buga gasar Zakarun Turai ta Uefa a kaka ta gaba kenan.

Kociyan ya ce : "A kowace kasa a duniya ranar Asabar ake yin wasan na karshe. Kuma muna nan a matsayi na shida duk yadda wasan ya kasance, sannan Palace ba ta da wata matsala.''

Ya kara da cewa :"A shekara bakwai da na yi a Ingila ban taba ganin yadda hukumomin wasan kasar ke taimaka wa kungiyoyin Ingila da ke wasan kofin Turai ba."

Sai dai kociyan ya nuna cewa ba wai yana neman hukumar gasar Premier ta dauke wasansu na ranar Lahadin ba ne, rana ta karshe ta gasar ta bana, yana mai bayyana lamarin da wanda ta faru ta kare.

Palace ta tsira daga gasar sakamakon nasarar da ta yi ta doke Hull ranar Lahadi da ci 4-0, inda kungiyar ta Sam Allardyce ta zama ta 13 a tebur.

Mourinho ya ce zai sa matasan 'yan wasa ne da yawa a karawar ta ranar Lahadi a Old Trafford, yana mai cewa yana fatan ba za a kashe shi ba idan aka ga zubin 'yan wasan da zai yi.

Ya ce yana fatan magoya bayan kungiyar za su goya musu baya, kuma su hada da hakuri kan rashin kwarewar 'yan wasan da za su gani.

Kuma ya yi fatan kociyan Palace Sam Allardyce, da 'yan wasansa Wilfried Zaha za su yi musu a hankali, kana kuma ya ajiye Christian Benteke a gida.

Shi ma Sam Allardyce ya ji takaicin rashin zuwan kungiyoyin Ingila matakin cin kofin Zakarun Turai, yana mai korafi irin na Mourinhon cewa hukumar Premier ba ta taimaka wa Mourinhon don ya samu damar zuwa gasar idan ya dauki Europa.

Ya ce: '' Haka ba za ta taba faruwa ba a wata kasa.''