Kane ya sake kafa tarihi a gasar Premier

Harry Kane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kane ne dan wasan da ya fi zura kwalla a gasar bara

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce dan wasan gaba na kungiyar Harry Kane, "na daya daga cikin 'yan wasan gaba mafi bajinta a duniya". Ya kuma ce kungiyar za ta rike 'yan wasanta masu bajinta a wanna kakar wasa.

Kane mai shekara 23, ya ci kwallo hudu a karawar da suka doke Leicester, da ci 6-1 ranar Alhamis, wanda hakan ya ba shi damar shiga gaban Romelu Lukaku da Alexis Sanchez, a yawan zura kwallo gasar Premier.

Image caption Kane na tsere da Lukaku da Sanchez a yawan zura kwallo

Pochettino ya ce, " Harry Kane dan wasa ne na musamman, kuma yana son Tottenham".

Dan wasan na Ingila, shi ne ya fi kowa zura kwallo a gasar ta bara, inda ya ci kwallo 25, kuma yana fatan maimaita bajintarsa, a kakar bana, inda kawo yanzu ya ci kwallo 26, yayin da ya rage wasa daya a kammala gasar.

Labarai masu alaka