Wenger: Za a san makomata bayan wasan FA

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wenger na fuskantar matsin lamba daga magoya baya

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce za a sanar da makomarsa a taron masu ruwa da tsaki, da kungiyar za ta yi bayan wasan karshe na kofin FA ranar 27 ga watan Mayu.

Kocin mai shekara 67, na Arsenal tun shekarar 1996, kuma kwantiraginsa da kungiyar zai kare a karshen kakar bana.

Wenger na fuskantar matsin lamba daga magoya bayan kungiyar, inda suke kiransa da ya yi murabus.

Wenger ya ce " Akwai batutuwa masu yawa da za a tattauna da taron. Daya daga cikinsu shi ne makomar koci".

Arsenal din dai, za ta kara da Zakarun Premier, wato Chelsea a wasan karshe na kofin FA a filin wasa na Wembley, kofi daya tilo da Arsenal din ke fatan samu a kakar wasa ta bana.

Labarai masu alaka