Sau bakwai Madrid ta ci La Liga a ranar karshe

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Madrid ce ta daya a kan teburi da maki 90

A ranar Lahadi aka karasa wasannin karshe a gasar cin kofin La Liga ta Spaniya ta 2016/17, inda aka fafata a karawa biyar, bayan da aka yi biyar a ranar Asabar.

Wasan da ya ja hankali shi ne wanda Real Madrid ta ziyarci Malaga ta kuma doke ta da ci 2-0 da wanda Barcelona ta karbi bakuncin Eibar ta kuma samu nasara da ci 4-2.

Real Madid ce ta kammala gasar bana a mataki na daya da maki 93 sai Barcelona ta biyu da maki 90, yayin da Atletico Madrid mai maki 78 ta kare a mataki na uku.

Da wannan nasarar da Madrid ta yi ya sa ta dauki kofin La Liga sau bakwai a ranar karshe da ake rufe gasar.

Ga jerin wasannin ranar karshe da Madrid ta lashe kofin La Liga

  1. 1932/32 (Barcelona 2 - 2 Real Madrid)
  2. 1964/65 (Sevilla 0 - 1 Real Madrid)
  3. 1971/72 (Real Madrid 4 - 1 Sevilla)
  4. 1979/80 (Real Madrid 3 - 1 Athletic)
  5. 2002/03 (Real Madrid 3 - 1 Athletic)
  6. 2006/07 (Real Madrid 3 - 1 Mallorca)
  7. 2016/17 (Malaga 0 -2 Real Madrid)

Labarai masu alaka