Guardiola ya kai Man City gasar Zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City ce ta uku a kan teburin Premier na bana, za kuma ta buga gasar Zakarun Turai ta badi

A kakar farko da Pep Guardiola ya jagoranci Manchester City ya kai ta gasar cin kofin zakarun Turai da za a yi a kakar 2017/18.

A ranar Lahadi City ta buga wasan karshe a gasar Premier ta bana, inda ta doke Watford da ci 5-0, kuma Kompany ya fara cin kwallo sai Aguero da ya ci biyu, Fernandinho da Jesus kowannensu ya ci guda-guda.

Da wannan sakamakon City ta kammala a wasannin bana na Premier a matsayi na uku da maki 78, wanda hakan ya sa za ta je gasar cin kofin Zakarun Turai ta badi kenan.

Guardiola wanda ya fara jan ragamar Man City a bana ya kasa lashe kofin zakarun Turai da na FA da kuma League Cup.

Shi kuwa kociyan Watford, Walter Mazzarri wanda zai bar kungiyar a bana ya sha ihu a wajen 'yan kallo, bayan da suka kasa taka rawar gani sannan su ne na 17 a kan teburi.

Labarai masu alaka