Real Madrid ta lashe kofin La Liga na bana

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ta dauki kofin La Liga na bana na kuma 33 junulla

Real Madrid ta dauki kofin La Liga na Spaniya na shekarar nan, bayan da ta ci Malaga 2-0 a wasan karshe da suka kara a ranar Lahadi.

Madrid din wadda ta buga wasa 38 a gasar ta bana ta hada maki 93, ta ci wasa 29 da canjaras shida aka doke ta sau uku, kuma ta ci kwallo 106 aka zura mata 41.

Wannan kuma shi ne kofin La Liga na 33 da ta dauka jumulla, wanda rabonta da shi tun na kakar 2011/12.

Yan zuma kuma Real Madrid za ta buga wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai da Juventus a ranar Asabar 3 ga watan Yuni a Cardiff.

Barcelona ce ta kammala wasannin La Liga na bana a mataki na biyu da maki 90 sai Atletico Madrid da maki 78.

ita kuwa Barcelona za ta buga wasan karshe a Copa del Rey da Deportivo Alaves a ranar Asabar.

Kungiyoyi uku da suka bar gasar La Liga ta shekarar nan sun hada da Sporting Gijon da Osasuna da Granada.

Labarai masu alaka