'Ba zan sayar da hannun jarin Arsenal ba'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta kasa samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta badi, bayan shekara 20 ana fafatawa da ita

Mutumin da ya mallaki hannun jari mafi yawa a Arsenal Stan Kroenke ya ce ba zai sayar da kason da yake da shi ba.

Kroenke wanda Ba'amerike ne, ya sanar da hakan a ranar Litinin, bayan da Alisher Usmanov ya yi masa tayin fam biliyan daya domin ya mallaki Gunners.

Dan Amurakar yana da kashi 67 cikin dari nahannun jarin Arsenal, shi kuma Usmanov yana da 30 cikin dari amma ba ya cikin mahukuntan da ke yanke shawara a kungiyar.

A ranar Lahadi Arsenal ta kasa samun tikitin shiga Gasar cin Kofin Zakarun Turai ta badi, wanda rabon da ta yi hakan tun shekara 20.

Usmanov ya fada a cikin watan Afirilu cewar dole Kroenke ya dauki alhakin dukkan sakamakon da Arsenal za ta fuskanta a cikin fili.

A ranar Asabar Arsenal za ta buga wasan karshe a Gasar cin kofin FA da Chelsea wadda ta lashe kofin Premier na shekarar nan.

Labarai masu alaka