Masu tsaron bayan Arsenal ba za su buga FA ba

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal za ta kece raini da Chelsea a wasan karshe a kofin FA a ranar Asabar a Wembley

Watakila wasu masu tsaron bayan Arsenal ba za su buga mata wasan karshe a kofin FA da za ta kara da Chelsea ba.

Da kyar ne idan Shkodran Mustafi zai buga karawar da za a yi a ranar Asabar sakamakon raunin da ya yi a wasa da Sunderland ranar Talata.

Shi kuwa Laurent Koscielny ba zai buga wasan karshe da za a yi a Wembley ba, sakamakon jan kati da aka ba shi a karawa da Everton.

Haka kuma koci Arsene Wenger ya ce raunin da Gabriel ya yi da alama mai muni ne.

Chelsea wadda ta dauki kofin Premier na bana za ta kece raini da Arsenal wadda ta kasa samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta badi, bayan shekara 20 tana halartar wasanni.