Moyes ya yi ritaya daga horar da Sunderland

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sunderland ce ta kare a mataki na karshe a gasar Premier da aka kammala

Kocin Sunderland, David Moyes ya yi ritaya daga jan ragamar kungiyar bayan da ta fice daga gasar Premier ta bana.

Wa'adin Sunderland na shekara 10 da ta yi a gasar ya zo karshe ne, bayan da Bournemouth ta doke ta a gasar Premier a watan Afirilu.

A ranar Litinin Moyes ya shaidawa shugaban kungiyar Ellis Short kan shawarar da ya yanke ta barin Sunderland din.

Moyes wanda ya horar da Everton da Manchester United ya karbi aikin jan ragamar Sunderland a watan Yunin bara, inda ya maye gurbin Sam Allardyce.

Sunderland ta kammala a mataki na karshe a gasar Premier ta shekarar nan da maki 24, bayan da ta ci wasanni shida kacal.