'Ba ma zawarcin Diego Costa'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea ce ta dauki kofin Premier na bana kuma na shida jumulla

Kungiyar kwallon kafa ta Tianjin Quanjian da ke China ta ce ba ta zawarcin Diego Costa kuma ba ta tuntubi wakilinsa watanni shida da suka wuce kan batun ba.

A watan Janairu aka yi ta rade-radin cewar Costa mai taka-leda a Chelsea mai shekara 28 zai koma China da murza-leda.

Costa ya taimaka wa Chelsea lashe kofin Premier na bana, inda ya ci kwallo 20 a wasannin shekarar nan.

Shugaban kungiyar ta China, Shu Yuhai ya fada a Janairu cewar dokar hukumar kwallon kafar kasar wadda ta ce 'yan wasa uku daga waje ya kamata a saka a fili ce ta kawo musu cikas.

Tianji ta samu gurbin shiga wasan gasar China ta Super League a bara, kuma Fabio Cannavaro shi ne kocinta.