Europa: United za ta kara da Ajax ranar Laraba

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Man United da Ajax za su buga wasan karshe na Europa a Stockholm a ranar Alhamis

Kungiyar Manchester United za ta kece raini da Ajax a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai na Europa a ranar Laraba.

Duk kungiyar da ta lashe kofin na Europa za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai ta badi kai tsaye.

Kungiyoyin biyu sun fafata sau hudu a gasar ta zakarun Turai, kuma kowacce ta ci karawa biyu.

Manchester United ta kare a mataki na shida a kan teburin Premier bana, yayin da Ajax ta yi ta biyu a gasar Netherlands.

Ga sakamakon haduwar da kungiyoyin biyu suka yi:

1976/1977

  • UEFA Cup Man Utd 2 - 0 Ajax
  • UEFA Cup Ajax 1 - 0 Man Utd

2011/2012

  • Europa League Man Utd 1 - 2 Ajax
  • Europa League Ajax 0 - 2 Man Utd

Labarai masu alaka