An dakatar da Koscielny buga wasa uku

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta kare a mataki na biyar a kan teburin Premier bana, za ta buga Europa a badi

Mai tsaron bayan Arsenal, Laurent Koscielny ba zai buga wasan karshe a kofin FA da kungiyar za ta kara da Chelsea a ranar Asabar ba.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ce ta ki amincewa da daukaka karar da Arsenal ta shigar kan jan katin da aka bai wa dan kwallon a wasa da Everton a ranar Lahadi.

An kori Koscielny daga filin wasa bayan da ya yi wa Enner Valencia keta a wasan karshe a gasar Premier ta bana da suka doke Everton 3-1.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da dan kwallon buga wasa uku, inda ba zai yi gumurzun da za a yi a ranar Asabar ba.

Haka kuma watakila Arsenal ta buga wasan na hamayya da Chelsea ba tare da Shkodran Mustafi ba.

Shi kuwa mai tsaron bayan Arsenal Gabriel wanda aka fitar daga fili sakamakon raunin da ya yi shi ma da kyar ne idan zai yi wasan.

Labarai masu alaka