An tabbatar da hukuncin daure Messi a gidan yari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A shekarar 2016 aka tuhumi Messi da mahaifinsa kan kin biyan kudin haraji

Wata babbar kotu a Spaniya ta tabbatar da hukuncin zaman gidan kaso na wata 21 da a baya aka yankewa dan kwallon Barcelona, Lionel Messi.

Sai dai kuma da kyar ne idan Messi kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Argentina zai yi zaman kason na wata 21.

A shekarar 2016 wata kotu a Spaniya ta tuhumi Messi da mahaifinsa Jorge Messi kan kin biyan haraji da ya kai fam miliyan 3.5.

Sai dai kuma daga baya aka rage hukuncin zaman yarin na Jorge Messi saboda ya biya wasu daga kudin harajin da ake tuhumarsu.

A dokar kasar Spaniya duk hukuncin da bai kai tsawon shekara biyu ba, za a iya yinshi na wucin gadi.

Yanzu haka za a mayar da hukuncin zuwa kotun farko da ke Barcelona wadda ta fara yanke wa'adin daure Messi wata 21 a gidan kaso.

Messi dai ya musanta aikata ba daidai ba, kuma ya ce babu abin da ke gabansa fiye da murza-leda.

Labarai masu alaka