Chelsea ta soke bikin lashe kofin Premier

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea ta lashe kofin Premier na bana kuma na shida jumulla

Chelsea ta ce ta soke bikin lashe kofin Premier da ta dauka a bana wanda ta shirya yi a ranar Lahadi, sakamakon harin ta'addanci da aka kai Manchester Arena.

Kungiyar ta ce bai kamata ta shirya wani biki a lokacin da ake tsaka da jimamin mutuwar mutane 22 da wasu ke kan gadon asibiti a harin da ya rutsa da su a ranar Litinin.

Tun farko Chelsea ta shirya zagaya birnin Landan a budaddiyar mota dauke da 'yan wasa da kofin Premier da ta ci da gurbin da za a saka na FA idan ta doke Arsenal a ranar Asabar.

Ita ma kungiyar Arsenal wadda za ta buga wasan karshe da Chelsea a Wembley ta ce ba za ta yi bikin lashe kofin FA ba idan har ta samu nasarar lashe shi.

Arsenal ta kare a mataki na biyar a kan teburin Premier da aka kammala a bana, hakan na nufin kungiyar za ta buga wasannin Europa na badi, bayan shekara 20 ana fafatawa da ita a Champions League.

Labarai masu alaka