Watakila kofin FA ne wasan Wenger na karshe

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ne karon farko da Arsenal ta kasa kammalawa a hudun farko a gasar Premier tun bayan shekara 20

Kocin Arsene Wenger ya ce bai sani ba idan wasan karshe na kofin FA da zai yi a ranar Asabar ko shi ne na karshe da zai yi a Gunners.

Sai bayan an kammala gasar cin kofin FA a ranar Asabar, mahukuntan Arsenal za su yi taro domin fayyace makomar kociyan.

Wenger ya fara horar da Arsenal a shekarar 1996, kuma a karshen kakar bana ne yarjejeniyarsa ke karewa a Arsenal.

A ranar Lahadi kocin ya ce rashin sanin makomarsa a Gunners na daya daga dalilin da ya sa kungiyar ta kasa taka rawar gani.

Wenger ya ce 'yana fatan ya ci wa Arsenal kofi, kuma abin da ya saka a gaba kenan'.