Man United ta samu tikitin Gasar Zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Man United ta kare a mataki na shida a kan teburin Premier na shekarar nan da aka kammala a ranar Lahadi

Manchester United za ta buga Gasar cin Kofin Zakarun Turai ta badi, bayan da ta doke Ajax da ci 2-0 a Stockholm.

United wadda ta ci kofin Europa na bana ta ci kwallon farko ta hannun Paul Pogba daga baya Henrikh Mkhitaryan ya kara ta biyu.

Da wannan nasarar ta United wadda ta yi ta shida a teburin Premier ta bana za ta buga Gasar cin Kofin Zakarun Turai ta badi kai tsaye kenan.

Haka kuma Jose Mourinho ya zama koci na farko da ya lashe kofin zakarun Turai na Uefa da na Europa sau bibiyu.

Labarai masu alaka