Totti zai rataye takalmansa ranar Lahadi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Totti ya fara yi wa Roma wasa yana da shekara 16 a Maris din 1993

A ranar Lahadi Francesco Totti zai yi ritaya daga murza-leda a kungiyar kwallon kafa ta Roma.

Totti mai shekara 40 wanda ya yi kakar wasa 24 a Roma zai zama daraktan kungiyar da zarar ya bar buga mata tamaula.

Ya fara yi wa Roma wasa a cikin watan Maris din 1993 a lokacin yana da shekara 16, ya ci kwallo 307 a fafatawa 783 da ya yi.

A ranar Lahadi za a rufe gasar Serie A ta Italiya ta shekarar nan, inda Roma za ta karbi bakuncin Genoa a ranar 28 ga watan Mayu.

Totti wanda ya lashe kofin duniya da tawagar kwallon kafa ta Italiya a 2006, ya ci Kofin Serie A daya da na kalubalen kasar biyu a Roma.

Labarai masu alaka