Ingila ta ki gayyatar Wayne Rooney

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wayne Rooney ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Inbgila wasa 119

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ba ta bai wa Wayne Rooney goron gayyata zuwa wasan da za ta yi da Scotland da Faransa ba.

Rooney wanda ya yi wa Ingila wasa 119, ya buga wa Manchester United fafatawa 15 a kakar bana.

Ingila za ta kara da Scotland a wasan shiga gasar cin kofin duniya a ranar 10 ga watan Yuni a Hampden Park.

Daga nan ne tawagar za ta buga wasan sada zumunta da Faransa a ranar 13 ga watan Yuni.

Ingila ce ta daya a kan teburin rukuni na shida da maki 13, yayin da Scotland ke matsayi na hudu da maki bakwai a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018..