Ronaldo ya ci kwallo 405 a Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo ya koma Real Madrid a shekarar 2009

Cristiano Ronaldo ya ci wa Real Madrid kwallo 405 a kakar wasa takwas da yake murza-mata leda.

Dan kwallon na Portugal ya ci 40 a wasannin shekarar nan, kuma kaka bakwai a jere yana cin fiye da 40.

Ronaldo ya ci kwallo 25 a La Liga da 10 a Gasar cin Kofin Zakarun Turai da hudu a Kofin Zakarun nahiyoyi da guda daya a Copa del Rey.

Real Madrid za ta buga wasan karshe da Juventus a Kofin Zakarun Turai a ranar 3 ga watan Yuni.

Dan wasan ya koma Madrid a shekarar 2009 daga Manchester United.

Ga jerin kwallayen da dan wasan ya ci a Madrid.

  • 2009/10 - 33
  • 2010/11 - 54
  • 2011/12 - 60
  • 2012/13 - 55
  • 2013/14 - 51
  • 2014/15 - 61
  • 2015/16 - 51
  • 2017/18 - 40

Labarai masu alaka