Kofin FA: Arsenal za ta kara da Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal tana da kofin FA guda 12, ita kuwa Chelsea tana da guda bakwai

Kungiyar Arsenal za ta fafata da Chelsea a wasan karshe a kofin kalubale na kakar wasan bana a Wembley a ranar Asabar.

Chelsea ce ta lashe kofin Premier da aka kammala na bana, yayin da Arsenal ta kare a mataki na biyar.

Arsenal ta lashe kofin FA sau 12, ita kuwa Chelsea tana da shi guda bakwai.

Sai bayan an kammala karawar ce mahukuntan Arsenal za su tattauna domin fayyace makomar Arsene Wenger a kungiyar.

Haka kuma za a tanadi matakan tsaro domin kaucewa abin da ya faru na harin kunar bakin wake a Manchester Arena a ranar Litinin.

Labarai masu alaka