Watakila a tuhumi Ronaldo da kin biyan haraji

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lokacin da 'yan wasan Real Madrid ke murnar lashe kofin La Liga wanda rabon da ta dauka tun 2012

Watakila a tuhumi dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo da laifin kin biyan haraji a Spaniya.

Masu shigar da kara sun mika takardu ga ofishin tara kudin haraji, wadanda za su fayyace ko za a tuhumi dan kwallon ko akasin hakan.

Rahotanni a Spaniya na cewa ana zargin Ronaldo mai shekara 33 da kin biyan harajin kudi fam miliyan 13 daga shekarar 2011 zuwa 2014.

Wasu takardun sirri da aka fitar a watan Disamba sun nuna yadda Ronaldo ya kaucewa biyan haraji a kudin da yake samu don amfani da hotunansa a ma'ajiyar da ya tanada a wajen Spain.

Ronaldo ya karyata aikat ba daidai ba.

Shi ma kocin Manchester United, Jose Mourinho yana cikin wadanda aka zarga, amma ya karya ta batun.

Labarai masu alaka