Man Utd: Valencia ya tsawaita zamansa

Antonio Valencia Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Valencia ne ya jagoranci kungiyar Manchester United a wasan Europa

Dan wasan baya na Man Utd Antonio Valencia ya sanya hannu a kwantiragin karin shekara daya da kungiyar, wanda hakan zai sa ya ci gaba da zama a old Trafford har 2019, kuma yana da zabin karin shekara daya.

Valencia, mai shekara 31, ya bugawa kungiyar United wasannin 43 da ta yi a kakar bana, ya kuma jagoranci kungiyar a matsayin kyaftin a wasan karshe na gasar Zakarun Turai ta Europa da suka doke Ajax.

Dan wasan wanda dan kasar Ecuador ne, ya koma Old Trafford da murza leda daga Wigan a shekarar 2009.

Ya ce, "Ina matukar farin cikin sabunta kwantiragina"

"Manchester United ta shiga rayuwata tun 2009. Ina so in mika godiyata ga manajan mu saboda kwarin gwiwar da ya bani a kakar wasa ta bana, na kuma tabbata za mu taka muhimmiyar rawa a kaka mai zuwa."

A watan Janairun da ya gabata ne United ta tsawaita wa Valencia kwantiragin shekara guda, a lokacin ta ce zai zauna a kungiyar har zuwa shekara ta 2018.

Labarai masu alaka