Man City Man City na dab da sayen Bernardo Silva daga Monaco

Bernardo Silva Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bernardo Silva ya ci wa Monaco kwallo 11 a kakar wasa ta bana

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City na dab da kulla kwanitiragi da dan wasan tsakiya na Monaco Bernardo Silva a kan kudi fam miliyan 43.

Ana sa ran dan wasan mai shekara 22 dan asalin kasar Portugal zai zo City ne idan aka bude kasuwar cinikin 'yan wasa ranar daya ga watan Yuli.

Silva dai ya yi wa wa Monaco wasa 58 a kakar bana, da suka hada da wasa biyu da kungiyar ta kara da City a gasar Zakarun Turai.

Ya kuma ci kwallo 11 sannan ya taimaka aka ci 12.

Ya yi wa kasarsa ta Portugal wasa 12, inda ya ci mata kwallo guda.

Manchester City dai ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta badi, bayan da ta kare Premier a matsayi na uku.

Labarai masu alaka