FA Cup: Ba tabbas kan makomata a Arsenal--Wenger

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kociyan Arsenal,Arsene Wenger, ya ce sai bayan zaman kwamitin gudanarwan Arsenal ranar Talata ne za a fitar da matsaya kan makomarsa a kungiyar

Duk da cewar ya ci kofin kofin FA a ranar Asabar, kociyan Arsernal,Arsene Wenge, ya ce babu tabbas kan makomarsa.

A bayanin da ya yi bayan lashe kofin FA dinsa na bakwai, Wenger ya ce za a fitar da matsaya kan makomarsa a kungiyar ne ranar Laraba ko Alhamis bayan zaman kwamitin gudanarwar Arsenal ranar Talata.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta lashe kofin FA din ne bayan ta doke Chelsea da ci 2-1 a wasan da aka buga a ranar Asabar a filin wasan Wembley.

Alexis Sanchez ne ya sha wa Arsenal kwallo na daya a minti 4 da fara wasa.

Amman bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Victor Mosee, dan Najeriyar da ke buga wa Chelsea ya samu jan kati lamarin da ya rage 'yan wasan Chelsea zuwa goma.

Duk da hakan Diego Costa ya rama wa Chelsea a minti na 76 da fara wasa.

Bayan minti uku da kwallon Diego Costa, Aaron Ramsey ya tura kwallon da Girou ya bugo masa cikin ragar Chelsea.

Wannan kofin FA din shi ne kofin FA na 13 da Arsenal ta ci.