Na ji takaicin rashin fara FA da ni - Fabregas

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fabregas ya koma Chelsea daga Barcelona a shekarar 2014

Cesc Fabregas ya ce ya ji takaicin rashin fara gasar cin kofin kalubale wanda Chelsea ba ta fara karawar da shi ba a ranar Asabar.

Arsenal ce ta doke Chelsea da ci 2-1, wanda hakan ya sa ta lashe kofi na 13 jumulla kuma na bakwai da Arsene Wenger ya dauka a tarihi.

Fabregas wanda ya zauna a benci a karawar ya shiga filin wasa bayan da aka dawo daga hutu a Wembley.

Dan kwallon ya buga wa Chelsea wasa 15 a kakar bana, hudu daga ciki a wasannin Premier Shida na karshe da kungiyar ta ci kofin bana.

Fabregas ya ce 'abin kunya ne da ba a fara karawar da shi ba domin yana kan ganiyarsa'.

Dan wasan wanda ya ci kofin FA da Arsenal a 2005, ya koma Chelsea daga Barcelona a shekarar 2014.

Labarai masu alaka