Ifeanyi Ubah ta ci Kano Pillars 2-0

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Ifeanyi Ubah ta yi wasa takwas ba tare da an doke ta a gasar Premier ta Nigeria ba

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi rashin nasara da ci 2-0 a gasar Premier Nigeria da ta ziyarci IfeanyiUbah a ranar Lahadi.

Mai masaukin bakin ta ci kwallayen biyu ne ta hannun Godwin Obaje, kuma shi ne aka zaba wanda yafi taka rawar gani a karawar.

Bayan da aka yi wasannin mako na 21, IfeanyiUbah ta buga karawa takwas a jere ba tare da an doke ta ba.

Ga sakamakon wasannin mako na 21 da aka buga ranar Lahadi:

  • Plateau Utd 1-0 Remo Stars
  • Gombe 1-0 Katsina
  • El-Kanemi 2-1 Rivers
  • Akwa Utd 3-0 ABS
  • Nasarawa 2-0 Wikki
  • Lobi 3-0 3SC
  • Tornadoes 3-0
  • Sunshine 1-0 Enyimba
  • Abia 4-0 Enugu Rangers