Ernesto Valverde ne zai zamo sabon kocin Barcelona

Ernesto Valverde Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabon Koci Ernesto Valverde ya taka muhimmiyar rawa yayin da yake wasa a kulob din Espanyol da kuma Athletic Bilbao

A na sa ran a ranar Litinin kulob din Barcelona zai sanar da nadin Ernesto Valverde a matsayin sabon kocin kungiyar bayan tafiyar Luis Enrique.

Tsohon dan wasan gaban Barca Valverde ya sanar a makon jiya cewa zai bar Athletic Bilbao bayan ya shafe shekara hudu yana jagorantar kungiyar.

Kocin mai shekara 53 zai maye gurbin Luis Enrique, wanda a watan Maris ya ce zai bar Barca a karshen kakar bana bayan ya yi shekara uku da su.

A wasan karshe da Enriqueya jagoranci Barcelona, kulob din ya doke Alaves da ci 3-1, inda hakan ya ba su damar daukar kofin Copa del Rey a ranar Asabar.

A ranar Litinin ne ake sa ran Shugaban kulob din Barcelona Josep Maria Bartomeu zai fitar da wata sanarwa kan batun.

Valverde ya yi wasa a Barcelona a tsakanin sheakarun 1988 zuwa 1990, inda ya ciyo mata kwallaye takwas a wasa 22 da ya buga.

Dan asalin kasar Spain, Valverde ya jagoranci Athletic Bilbao ta samu matsayi na bakwai a kakar La Ligar bana, yayin da Barcelona ta kare a mataki na biyu, Real Madrid kuma ta zama zakara.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba