Joe Hart ya bar Torino - ko ina zai koma?

Joe Hart Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Joe Hart ya yi wa Torino wasa 36 a kakar bana

Golan Manchester City Joe Hart ya ba da tabbacin cewa zai bar kulob din Torino, bayan a zauna a kulob ɗ in da ke ƙasar Italiya a matsayin aro har tsawon kaka daya.

Hart mai shekara 29 ya koma kulob ɗin ne a watan Agustan bara, bayan da Kocin City Pep Guardiola ya ba shi zabin yin hakan.

Kocin Torino Sinisa Mihajlovic ya ce ya so dan wasan ya ci gaba da wasa da su, amma kulob din ba shi ƙarfin sayensa.

"Na gode Torino, Ina alfahari da na yi wasa a kulob din da ya fita daban da saura," inji golan Ingilan kamar yadda ya bayyana a shafinsa na sada zumunta ranar Litinin.

"Zan dawo don ganawa da ku duka, sai wata rana, ina muka fatan kakar wasa mai kyau."

An ƙare Gasar Serie A, Torino tana a matsayi na tara, bayan wasanta na karshe da ta doke Sassuolo da ci 5-3.

Hart ya lashe kofuna 68 a kasar Ingila kuma ana danganta dan wasan da kolob da dama na Gasar Firimiya da kuma Turai..

Labarai masu alaka