Ernesto Valverde ne sabon kocin Barcelona

Valverde Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ernesto Valverde ya jagoranci kulob din Athletic Bilbao har tsawon shekara hudu

Kulob din Barcelona ya nada Ernesto Valverde a matsayin sabon kocinsa har tsawon shekara biyu.

A makon jiya ne kocin wanda tsohon dan wasan Barcelona ne ya ce zai bar kolub din da yake jagoranta Athletic Bilbao bayan ya shafe shekara hudu a can.

Shugaban kulob din Barcelona Josep Maria Bartomeu ya yaba da kwazo da gogewar Valverde, inda ya bayyana shi da "wanda ya iya renon kananan 'yan wasa kuma tsohon dan wasan Barca"

Sabon kocin, mai shekara 53, ya maye gurbin Luis Enrique, wanda a watan Maris ya ce zai bar Barca a karshen kakar bana bayan ya yi shekara uku da su.

A wasan karshe da Enriqueya jagoranci Barcelona, kulob din ya doke Alaves da ci 3-1, inda hakan ya ba su damar daukar kofin Copa del Rey a ranar Asabar.

Valverde ya yi wasa a Barcelona a tsakanin sheakarun 1988 zuwa 1990, inda ya ciyo mata kwallaye takwas a wasa 22 da ya buga.

Dan asalin kasar Spain, Valverde ya jagoranci Athletic Bilbao ta samu matsayi na bakwai a kakar La Ligar bana, yayin da Barcelona ta kare a mataki na biyu, Real Madrid kuma ta zama zakara

Labarai masu alaka