Roma ta sallami kocinta Luciano Spalletti

Spalletti Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Luciano Spalletti ya jagoranci Roma tsakanin 2005 zuwa 2009

Kolob din AS Roma ya sallami kocinsa Luciano Spalletti bayan ya kammala Gasar Serie A ta bana a mataki na biyu.

Sanarwar sallamar ta zo ne bayan da kulob din ya doke Genoa da ci 3-2 ranar Lahadi.

Spalletti ya koma Roma ne a karo na biyu a watan Janairun shekarar 2016.

Shugaban Roma Jim Pallotta ya ce "muna godiya ga Spalletti bisa yadda ya yi aiki tukuru tun bayan komawarsa jogorancin kulob din."

Ya ci gaba da cewa: "a karkashin jagorancinsa kulob din ya samu maki mai yawa kuma ya zura kwallaye a raga fiye da kowane lokaci a tarihin Roma. Muna yi wa Luciano fatan alheri a duk abin da zai yi a nan gaba"

Spalletti, mai shekara 58, ya jagoranci Roma tsakanin shekarar 2005 zuwa 2009, sau biyu yana lashe kocin Coppa Italia, gabanin ya ajiye aiki ya koma Zenit St Petersburg na kasar Rasha.

Kocin wanda kwangilarsa da Roma ta kare a kakar bana, yana shan suka game da tsawon lokacin da yake sanya fitaccen dan wasan kulob din Francesco Totti ya yi wasa.

Totti, mai shekara 40, ya yi ritaya daga tamaula ranar Lahadi bayan ya shafe shekara 25 a Roma.