Wenger ya gana da shugaban Arsenal kan makomarsa

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta doke Chelsea da ci 2-1 ranar Asabar, inda ta lashe kofin FA

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya gana da mutumin da ya mallaki kulob din, Stan Kroenke, game da makomarsa ranar Litinin.

Sai dai ba a san ko sun yanke wani hukunci ba tukuna, amma ana da tabbacin cewa makomar Wenger a kulob din tana hannunsa da Kroenke da kuma daraktocin kulob din wadanda za su yi wani taro ranar Talata.

Har ila yau, Wenger, mai shekara 67, ya gana da shugaban zartarwan kulob din Ivan Gazidis a ranar Litinin.

Mista Gazidis ya sha bayyana goyon bayansa ga kocin da kuma ba shi tabbacin cewa zai samar masa da duk abin da zai bukata don ya lashe Gasar Firimiya.

A ranar Laraba ne kulob din zai fitar da sanarwa game da makomar kocin.

Arsenal ta yi rashin nasara a wasanni 12 tsakanin ranar 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Afrilu, ciki har da wasan Bayern Munich ta doke su da ci 10 - 2 (jimulla) a Gasar Zakarun Turai.

Sai dai Arsenal ta doke Chelsea ranar Asabar, inda ta lashe kofin FA.