Wenger zai kara shekara biyu a Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal za ta buga gasar Zakarun Turai ta Europa ta badi

Arsene Wenger ya amince zai ci gaba da jan ragamar Arsenal zuwa shekara biyu.

A ranar Litinin ne Wenger da mahukuntan Arsenal suka zauna taro domin fayyace makomar kocin, kuma sai a ranar Laraba ne kungiyar za ta sanar da yarjejeniyar da suka cimma.

Arsenal ta kare a mataki na biyar a kan teburin gasar Premier da aka kammala, inda za ta buga gasar Zakarun Turai ta Europa a badi.

Kuma wannan ne karon farko da Arsenal ta kasa kammala gasar Premier a cikin 'yan hudun farko tun lokacin da Wenger ya fara jan ragamar kungiyar a shekarar 1996.

Sai dai kuma Wenger wanda ya ci kofin Premier hudu a Gunners ya lashe kofin FA a ranar Asabar bayan da ya doke Chelsea da ci 2-1 a Wembley.

Hakan ne ya sa ya lashe kofin FA na bakwai kuma na 13 da Arsenal ta ci a tarihi.

Labarai masu alaka