Za mu rike Aguero - Khaldoon

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aguero ya ci kwallo 21 a wasannin Premier 31 da ya buga wa City a 2016/17

Shugaban kungiyar Manchester City, Khaldoon Al Mubarak, ya ce ba sa tantamar makomar Sergio Aguero a kungiyar.

A watan Fabrairu Gebriel Jesus ya maye gurbin Aguero a buga wa City wasanni, dalilin da ya sa aka dinga rade-radin cewar zai bar Ettihad a karshen kakar nan.

Mubarak ya ce 'ya dade yana jin zantuttuka kan makomar Aguero a City, amma daya ne daga fiattun 'yan wasa a duniya kuma wajibi ne mu rike shi'.

Aguero ya ci kwallo 33 a wasa 45 da ya buga a kakar nan, kuma sai a shekarar 2020 ne yarjejeniyarsa za ta kare a Ettihad.

Dan kwallon na tawagar Argentina ya fada a watan Maris cewar baya son ya bar Manchester City da murza-leda.

Labarai masu alaka