Man City na daf da sayen Moraes

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Juma'a Manchester City ta amince da Willy Caballero ya bar kungiyar

Manchester City na daf da sayen mai tsaron ragar Benfica, Ederson Moraes kan kudi fam miliyan 33.

A watan Maris din bara Moraes mai shekara 23, ya fara tsaron ragar Benfica, ya zuwa yanzu ya yi wasa 37 a kungiyar da ta lashe kofin Portugal na bana.

Tun a ranar Lahadi a lokacin da Benfica ta doke Vitoria Guimaraes 2-1, Moraes ya ce wasansa na karshe ke nan a kungiyar.

Matashin dan kwallon tawagar Brazil wanda har yanzu bai buga mata tamaula ba, yana daga cikin wadanda aka gayyata wasan sada zumunta da za ta yi da Argentina da Australia a nan gaba.

Kocin City, Pep Guardiola ya dade yana son daukar Moraes a baya can, dalilin da ya sa ya bar Willy Caballero ya bar Ettihad domin dan kwallon ya samu gurbin zama a kungiyar.