An ci kwallo 415 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption A ranar Lahadi aka buga wasannin mako na 21 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Kwallo 415 aka ci a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka yi wasannin mako na 21 a ranar Lahadi.

Bayan da aka yi wasa 210 a gasar, an ci kwallo 23 a fafatawa 10 da aka buga a ranar Lahadin.

Kuma dukkan kungiyoyin da suke gida ne suka lashe wasanninsu.

Karawar da aka fi zura kwallo a raga ita ce wadda Abia Warriors ta doke Enugu Rangers da ci 4-0.

Ga 'yan wasan da suke kan gaba a cin kwallayen:

  • Stephen Odey na Mountain of Fire 14
  • Samuel Mathias El-Kanemi Warriors 11
  • Sunday Adetunji Abia Warriors 11
  • Alhassan Jibrin Akwa United 10
  • Godwin Obaje IfeanyiUbah 9