Mahrez yana son barin Leicester City

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mahrez ya koma Leicester City a shekarar 2014 daga Le Havre

Riyad Mahrez ya ce yana son ya bar kungiyar kwallon kafa ta Leicester City.

Mahrez ya ce ya amince ya ci gaba da buga wa Leicester wasa zuwa shekara daya, bayan tattaunawa da ya yi da shugaban kungiyar a lokacin da suka ci Premier a bara.

Dan kwallon tawagar Algeria mai shekara 26, ya koma Leicester da taka-leda a shekarar 2014 daga Le Havre kan kudi fam 400,000.

Mahrez ya buga wa Leicester City wasa 48 a kakar bana, kuma shi ne ya lashe kyautar dan kwallon da babu kamarsa a Premier a 2016.

Dan wasan ya ci kwallo 10, ya kuma taimaka aka ci bakwai a wasannin da Leicester ta yi ta 12 a gasar Premier da kaiwa karawar daf da kusa da karshe a Gasar cin Kofin Zakarun Turai.