United za ta sake hana Madrid daukar De Gea

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption De Gea bai buga wa United wasan Europa da ta kara da Ajax a ranar 24 ga watan Mayu ba

Manchester United na fatan sake dakile zawarcin da Real Madrid za ta yi wa mai tsaron ragarta David de Gea a bana.

A shekarar 2015 Real Madrid ta cimma yarjejeniyar daukar golan na United mai shekara 26.

A lokacin Madrid ta ci karo da tsaiko bayan da ta kasa hada takardun da suka dace kan cinikin dan kwallon.

Masu sharhi da bayanai na hangen watakila Real Madrid ta sake yunkurin sayen golan dan kasar Spaniya.

United ta saka Sergio Romero a ragarta a madadin De Gea a wasan karshe a Kofin Zakarun Turai na Europa da ta ci Ajax 2-0.

Labarai masu alaka