Kungiyoyi na zawarcin Ibrahimovic - Raiola

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ibrahimovic ya kwallo 17 a fafatawa 28 da ya yi wa Manchester United

Wakilin Zlatan Ibrahimovic, ya ce kungiyoyi da dama na son daukar dan kwallon, amma ba su yanke shawara ba a kai.

Mino Raiola ya ce suna ta samun karin kulub-kulob da suke zawarcin Ibrahimovic daga wurare da yawa.

A ranar 30 ga watan Yuni ne yarjejeniyar Ibrahimovic za ta kare da United, kuma har yanzu bai amince ya tsawaita zamansa a Old Trafford ba.

Raiola ya ce 'ya dace su tattauna da United domin fayyace idan dan wasan yana da daraja a wajensu'.

Ibrahimovic ya koma United da murza-leda a bara bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris St-Germain.

Dan wasan na yin jinyar raunin da ya ji a watan Afirilu, inda ake fata zai warke kafin fara gasar Premier ta badi.