De Rossi ya tsawaita zamansa a Roma

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daniele de Rossi da Francesco Totti sun yi wa Roma wasa 1347 su biyun

Kyaftin din Roma, Danielle de Rossi ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a kungiyar zuwa shekara biyu.

Rossi ya cimma yarjejeniyarce kwanaki uku, bayan da Francesco Totti ya yi ritaya daga buga wa kungiyar tamaula.

De Rossi zai karbi fam miliyan 5.24 a shekara, wanda hakan ya sa ya zama dan kwallon da ya fi karbar albashi a Serie A.

Dan kwallon mai shekara 33 ya yi wasa 561 tun lokacin da ya fara buga wa Roma tamaula a shekarar 2001.

A ranar Lahadi Totti ya yi ritaya a Roma, bayan da ya yi mata wasa 786, zai kuma zama daraktan kungiyar.

Labarai masu alaka